1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Al'ummar kan iyakokin Nijar na fama da hare-hare

August 15, 2024

Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun ce 'yan ta'adda sun halaka fararen hula 15 yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu kauyuka da ke yankin kan iyakar kasar da Burkina Faso.

Wasu daga cikin barnar da 'yan ta'adda ke yi a Nijar
Wasu daga cikin barnar da 'yan ta'adda ke yi a Nijar Hoto: Boureima Hama/AFP

'Yan bingida sun saba kai hare-hare a iyakokin Mali da Burkina Faso da kuma Nijar. Ko a ranar Talatar da ta gabata ma, 'yan ta'addan sun kashe wani mutum guda a Tillaberi tare da raunata wasu mutum uku kusa da garin Chatoumane, wanda daga bisani sojojin Nijar din suka maida martani ga ayyukan 'yan ta'addan.

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe sojoji a yankin Tillaberi na Nijar

Sanarwar hukumomin Nijar ta ce 'yan ta'addan sun mayar da yankin Mehana a matsayin tungar masu ikrarin jihadi na IS da ke alaka da kungiyar Al-Qaeda a yakin Tallebri da ke kan iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso.

Karin bayani: Nijar: Cece-kuce da UNDP kan binciken tsaro

Shugabannin mulkin sojin Nijar da suka karbi mulki a shekarar da ta gabata sun bayyana matsalar tsaro a matsayin dalilan hambarar da gwamnatin farar hula, amma wannan matsalar ta tsaro na ci gaba da kasancewa babban kalubale ga hukumomin kasar.