1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar kasar Somaliya na bukatar agajin gagawa.

Binta Aliyu Zurmi
April 11, 2023

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nemi kasashen duniya da su taimaka wa kasar Somaliya bisa halin kunci da al'ummar kasar ke ciki da ya samo asali daga matsanancin fari da suke fama da shi.

Somalia Mogadischu Besuch UN-Generalsekretär Guterres
Hoto: FEISAL OMAR/REUTERS

Antonio Guterres wanda ya kai ziyarar gani da ido a kasar da ke gabashin Afirka ya ce, Somaliya na cikin wani hali da ke bukatar agajin gagawa a daidai lokacin da suke kuma fama da ayyukan 'yan ta'adda.

A wata ganawa da manema labarai da ya yi tare da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmoud, Guterres ya ce, ya je kasar ce domin ya gani da idonsa ya kuma sanar wa duniya halin da al'ummar Somaliya ke ciki.

Al'umma a Somaliya dai na a cikin wani hali, inda aka tabbatar da akwai sama da mutane miliyan 6 da ke fama da matsananciyar yunwa, halin da ba a taba ganin irin shi ba a tarihin farin da kasar ta shiga a baya.