1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Al'ummar Mozambique na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

October 9, 2024

An bude rumfunan gudanar da babban zaben shugaban kasa da na gwamnonin larduna har ma da na 'yan majalisar dokoki a kasar Mozambique.

Dan takarar gwamna a lardin Tete Carlos Monteiro Chataica jim kadan da kada kuri'a a Mozambique.
Dan takarar gwamna a lardin Tete Carlos Monteiro Chataica jim kadan da kada kuri'a a Mozambique.Hoto: Jovenaldo Ngovene/DW

Shugaba mai barin gado Filipe Nyusi wanda yayi zangon mulkin biyu na shekara 10 a kasar ta Mozambique na daga cikin wadanda suka fara kada kuri'a, a zaben da ake hasashen jam'iyya mai mulki ta Frelimo ka iya lashe zaben. Jam'iyyar FRELIMO mai mulki ta tsayar da Daniel Chapo mai shekaru 47 a matsayin dan takararta yayin da zai fafata da 'yan adawa guda uku da suka hada da Ossufo Momade da Lutero Simango da Venâncio Mondlane.

Karin bayani: Zabe ya gudana salin-alin a kasar Mozambik 

Mutane miliyan 17 ne suka yi rajistar kada kuri'a daga cikin al'ummar kasar miliyan 33 wadanda suka fuskaci yakin basasa na tsawon shekaru 15 da aka kawo karshensa a 1992, kazalika a baya bayannan kasar ta sake fadawa tashin hankalin masu ikirarin jihadi a lardin Cabo Delgado, wanda ya raba mutane sama da miliyan 1.5 da muhallansu.