1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Ambaliya: An yi asarar dukiya a Najeriya

Aliyu Muhammad Waziri GAT
September 18, 2018

A Najeriya ruwan sama mai yawa da aka samu a garin Bauchi da wasu kananan hukumomi a jihar, ya haddasa ambaliya wacce ta lalata gidaje, wuraren ibada da na kasuwancin jama’a da dama.

Katsina Flut Nigeria
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Yanzu haka jama’a da dama na cikin wani mawuyacin yanayi bayan da suka yi asarar gidajensu da ma dukiyoyi masu tarin yawa, lamarin da ya jefa su cikin kaka-ni-ka yi. Kimanin gidaje dubu daya da tara ne dai wannan ambaliya ta lalata yayin da wuraren kasuwancin jama’a da na ibada da suka hada da masallatai da coci adadinsu ya kai sittin da bakwai da wannan ambaliya ta shafa.


Tuni dai gwamnatin jihar Bauchi ta nada kwamiti da ta dora wa alhakin zagawa da kididdige irin barnar da ambaliyar ta yi don tallafa wa wadanda suka yi asara. To sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba kasancewa wannan ambaliya ba ita ce ta farko da aka samu a Bauchin ba, domin ko mako biyu da suka wuce an samu wata ambaliyar da itama ta janyo asara mai tarin yawa amma har yanzu babu wani tallafi da mutanen da lamarin ya shafa suka samu daga wurin gwamnatin duk kuwa da ikirarin gwamnatin na cewa ta tallafa musu.

Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis


Yanzu dai mutanen da suke cikin wannan yanayi na rashin matsugunin, babban fatansu shi ne samun daukin gaggawa daga gwamnatin jihar Bauchi.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani