1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Borno: Amai da gudawa sakamakon ambaliya

September 20, 2022

Bayan da cutar amai da gudawa wato cholera ta hallaka sama mutane 50 a Borno Najeriya, hukumomi a jihar na neman taimakon kungiyoyin agaji wajen ganin an dakile yuduwar cutar tsakanin al'umma.

Najeriya | Ambaliyar Ruwa
Jihohi da dama na Najeriya, na fama da ibtila'in ambaliyar ruwaHoto: DW

Yayin da ake alakanta ibtila'in ambaliyar ruwan da barkewar cututtuka, ana samun karuwar barazanar amabliyar a jihohin Borno da Yobe wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi. Hukumar Lafiya ta jihar Bornon dai ta tabbatar da mutuwar mutane sama da 50, inda sama da mutane 700 kuma suka kamu da cutar amai da gudawa wato cholera a kanana hukumomi bakwai na jihar da kuma hukumomi suka ce tana bazuwa tamkar wutar daji. A cewar hukumomin jihar Bornon dai, kimanin mutane miliyan guda ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta amai da gudawa in har ba a samu daukin da ya kamata ba.

Dubban al'umma a jihar Borno, na gudun hijira sakamakon hare-haren Boko HaramHoto: Gilbertson/ZUMAPRESS/picture alliance

Cikin wuraren da wannan cuta ta bulla har da daya daga cikin sansanonin da ake ajiye mayakan Boko Haram da suka tuba, inda aka ruwaito mutum biyu daga cikinsu sun rasa rayukansu. Wannan ne ya sa hukumomi a jihar suka tashi tsaye domin magance yaduwar cutar, tare da neman taimakon kungiyoyin agaji da hukumomi na Majalisar Dinkin Duniya domin ganin an rage barnar da cutar ke yi koma dakile ta baki daya. Tuni dai al'umma suka fara nuna damuwa sakamakon illar da cutar ke yi, musamman ga kanan yara da kuma mata wanda ba su fita daga kangin da suka shiga na hare-haren Boko Haram da ya sahfi miliyoyin mutane a Najeriyar ba. Masana dai na ganin cewa matukar ana son a magance matsalar wannan cuta ta amai da gudawa, sai dole an magance matsalar dumama ko sauyin yanayi da kwararowar hamada.