Nijar:Ruwan sama sun kashe mutum 33
August 13, 2020Talla
Sama da gidaje dubu tara suka rushe a sakamakon ruwan ,da a wasu yankunan a cikin shekaru 40 ba a taba samun saukar daminar kamar haka ba. Jihohin da suka fi shafuwa sun hada da Maradi da Tahoua da Tillaberi da Dosso da ke a yankin yammacin kasa. Domin kawo dauki ga wadanda lamarin ya rutsa da su gwamnatin ta fara rarraba kayan abinci da sabulun wanka da tufafi da barkuna rufa ga jama'ar.