1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iAfghanistan

Afghanistan: Ambaliya ta halaka mutane

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 16, 2024

Mahukuntan Taliban da ke mulki a Afghanistan, sun sanar da cewa mamakon ruwan sama a gabashin kasar ya halaka kimanin mutane masu yawa da kuma jikkata wasu da dama.

Afghanistan | Ambaliya | Kisa
Ambaliyar ruwa ta halaka mutane da dama a AfghanistanHoto: Shafiullah Kakar/AP/dpa/picture alliance

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wasau mutane biyar 'yan gida daya, wadanda suka rasu sanadiyyar ruftawar da ginin gidansu ya yi a kansu a gundumar Surkh Rod kamar yadda kakakin gundumar Sediqullah Quraishi ya tabbatar. Kimanin gidaje 400 da kuma falwayoyin wuta 60 ruwan saman ya lalata a yankunan Nangarhar da Quraishi said, yayin da aka samu daukewar hasken wutar lantarki a manyan birane da dama ciki hadar da  Jalalabad.