Halitta da Muhalli
Ambaliya ta mamaye tituna da gidaje a Legas
June 30, 2026
Talla
Ko da yake kawo yanzu babu rahoton rasa rai, amma mazauna wasu unguwanni sun ce ambaliyar ta tilasta wa mutane amfani da kwale-kwale domin ficewa daga gidajensu da ambaliyar ta mamaye.
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa ana sa ran za a ci gaba da samun ruwan sama a kwanaki masu zuwa, lamarin da ka iya haddasa ƙarin ambaliya musamman a yankunan da ke bakin teku da kuma ƙananan wurare.
Masana sun ce yawaitar ambaliya a Legas na da nasaba da mamakon ruwan sama, ƙarancin magudanan ruwa, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba da kuma saurin faɗaɗar birnin.