Nijar: Mutane sun mutu sakamakon ambaliya
October 8, 2022Talla
Adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunan ambaliyar ruwa da ke addabar Jamhuriyar Nijar sun kai 192 kamar yadda hukumomin agajin kasar suka bayyana.
Hukumomin sun ce mamakon ruwan saman da aka fuskanta daga farkon watan Yunin wannan shekara ya yi dumbin illa wa kaddarorin jama'a da gonakai baya ga rugujewar gidaje inda mutane dubu 263 suka rabu da gidajensu.
Yankunan Maradi da Zinder da Dosso da Tahoua na daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi kamari in ji hukumomin kasar. Ko a shekarar da tagabata hukumomin agaji sun ce an samu mutane 70 da suka mutu wasu akalla dubu 200 suka rasa matsugunansu sakamakon mummunan ambaliya.