Ambaliya ta yi ta'adi mai yawa a Jamhuriyar Nijar
August 29, 2025
A Jamhuriyar Nijar kwamitin da ke sa ido kan rigakafi da matsalar ambaliyar ruwa na kasa ya ce ambaliyar bana da ta shafi kananan hukumomi sama da 90, ta lalata gidaje dubu 15 da 177 kai tsaye,wanda haka ya kai ga shafuwar mutane sama da dubu 100 a fadin kasar. A zama na biyu da kwamitin ya yi ya sanar cewa ya zuwa ranar 18 ga watan Agusta, gidaje 6,577 suka ruguje sakamakon ambaliyar wanda hakan ya shafi mutane dubu 46 da 957 inda suka samu tallafi na abinci a cewar kwamitin wanda ya kunshi ton 657 da digo bakwai na hatsi wanda ya ce za a ci gaba da rabon kayan don biyan sauran bukatun.
Sai kuma wannan zaman a uku na ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, kwanaki 10 ke nan bayan zaman a farko, kwamitin da ke kula da hanyoyin rigakafi sa ido kan batun ambaliyar ruwa na kasa na CNPGI, ya gudanar da taronsa karo na uku a karkashin jagorancin ministan kula da fannin gine-gine da samar da ababen more rayuwa, Kanar-Major Salissou Mahaman Salissou, inda ya zuwa yanzu matsalar ambaliyar ta shafi yankuna 551 a cikin kananan hukumomi 95, wanda ya shafi gidaje dubu 15 da 177 kai tsaye, inda lamari ya taba mutane kimanin dubu 110 da mutun 346 a fadin kasar.
Sai dai da yake Magana Soumaila Amadou, wanda shi ma ya girka wata kungiya ta zaburar da matasa zuwa ga noma a yankin Damagaram, ya ce ala tilas sai fa a tashi tsaye wajen fadakar da al'umma sauyin yanayi da illolinsa.
Minista Kanar-Major Salissou Mahaman Salissou, da ya jagoranci zaman kwamiti karo na uku, ya ba da tabbacin cewa gwamnati zai ba da tallafin ga ainahin wadanda sune wannan iftila'I ya shafa inda ya ce mutane su kiyaye wajen nuna gaskiya yayin ba da tallafin.