1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iAsiya

Ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Indonesiya

April 4, 2021

Zabtarewar kasa da ambaliyar ruwa sun yi sanadiyar halaka mutane da dama a kasar Indonisiya yayin da wasu dubbai suka tagaiyara.

Indonesien | Schäden nach Hochwasser
Hoto: Ola Adonara/AP/picture alliance

Wata zaftarewar laka da ambaliyar ruwa da aka samu a Indonisiya, sun yi sanadiyar hallaka mutane kusan 50 yayin da wasu duban suka rasa muhallansu.

Wani ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya a tsakiyar daren jiya shine ya haddasa balahirar, ambaliyar ta tafi da gadoji da ma gidajen al'umma da kawo yanzu ba a tantance yawansu ba.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta kasar Raditya Jati ya ce  jami'ansu gami da taimako yan sa kai sun sami nasarar ceto mutane da dama tare da zakulo wasu gawawwaki.