Ambaliya a Jamhuriyar Nijar
June 15, 2017A yayin wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo cushewar gadoji da ke fitar da ruwan sama zuwa tabakunan bayan gari ya saka faragaba na fuskantar ambaliyar ruwa a zukatan dubban magidanta a wasu sassan birnin Damagaram.
Hakika wannan fargaban fuskantar matsalar ambaliyar ruwa da dubban wasu mazauna birnin Damagaram suka fada tuni hadarin na daren Talata wayewar Laraba ya hadasa mummunar ambaliya a birnin Yamai tare da hallaka mutane 9 kamar yadda sakamakon wucin gadi na hukumomi ya nuna bayan kuma asarar kaddarori mai yawa.
Tuni dai gwamnatin kasar da abokan hulda suka bayana cewar mutane dubu 106 ne ke kan hanyar fuskantar ambaliyar a sakamakon cushewar magudanan ruwa da gine hanyoyi ba a kan ka’ida ba inda a Damagaram wasu mazauna birnin da wannan matsala ta shafa suka fara kokawa tare da zargin hukumomi da aikin ina ruwana.
Dokta Mahaman Bashir Sabo shi ne shugaban majalisar wakilan da’ira da nauyin aikin yasar gadojin game da korafin talakawan da fargaba na ambaliyar ruwan ta mamaye, cikin hanzari ya mayarv da martini kimanin milyar 3,6 na CFA kwatankwacin millions 6,5 na dollar Amirka ake hasashen sakawa a fanin aikin taimakon agajin gaugawa awanan shekara.