Ambaliyar ruwa a Jamus saboda canjin yanayi
June 5, 2013Dubban sojoji ne dai gwamnatin Jamus ta tura domin taimaka wa jama'ar da ke zaune a yankunan kudanci da gabashin kasar da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da ta rutsa da wasu kasashen Turai cikinsu har da Chek da Austriya. To ko ya ya girman barnar da wannan bala'i ya yi i?
Da kashi daya daga cikin dari ne dai Jamus ta samu habbakar tattalin arziki a watannin ukun farko na shekarar 2012- abin da ya sa aka kyautata fatan samun kari a watannin uku da ke biye. To amma sai gashi ba zato ba tsammani ruwan sama da ake tafkawa kamar da bakin kwarya da ambaliyar da ta biyo bayansa ya katse wannan hanzari duba da asarar da wannan bala'i ya haifar. Akan haka ne Alexander Schumann, shugaban kungiyar aikin masana'antu da kasuwanci a Jamus ke cewa:
"Abin farin ciki shi ne cewa muna da wata dama ta cimma fatanmu . To amma idan mutun ya dubi yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa zai gano cewa wannan ba abu ne mai sauki ba. Da farko ya kamata a kimanta irin barnar da wannan bala'i ya yi da kuma irin tasiri da zai yi akan ci-gaban da aka samu.
Akwai kuma kamfanoni da dama da wannan bala'i ya shafa .Wadadan sun hada ne da kamfanin Krones da ke sarrafa kwlabe wanda ya dakatar da aikinsa a yankin Uppper Bavariya kasancewar ma'aikatansa sun kasa zuwa aiki. Haka ma lamarin ya kasance a garin Zwickau da ke yankin Saxony inda kamfanin kera motocin VW shi kuma ya dakatar da aiknsa. Gunter Sandmann shi ne kakakkin kamfanin na VW.
Ya ce: "Bayan afkuwar wannan bala'i a ranar Lahadin da ta gabata ba mu yi wata-wata ba muka kira jami'an ceto.A ranar Litinin ne kuma muka tsai da shawarar dakatar da aikin safe a sakamakon lalacewar hanyoyin da ke kaiwa kamfanin."
Hakazalika ambaliyar ta kuma janyo tarnaki ga harkokin rayuwa a kasar Austriya sakamakon tunbasar kogin Danube- abin da kafafen yada labaru suka kira "Tubasar ta karni na 21" wadda kuma baa taba ganin irinta ba tun daga shekarar 2002. Mutane 10 ne dai aka tabbatar wannan bala'i ya rutsa da rayukansu aJamus a baya ga wasu kuma su bakwai da suka mutu a kasar Chek. Akwai kuma mutane tara da ba a san makomarsu ba a kasashen Austriya da Swizerland. Yayin ziyarar da ta kai a yankunan da bala'in ambaliyar ruwa ya shafa shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi alkawarin ba da taimkon kudi ga wadanda bala'in ya shafa ba da wata-wata ba. Merkel ta ce tuni gwamnatin Tarayya ta kebe Euro miliyan dari domin ba da wannan taimako daidai wa daida ga yankunan Bavariya da Saxony da Thueringen da bala'in ya shafa. Shugaban kasar Jamus, Joachim Gauck shi kuma ya mika godiyarsa ga 'yan kwana-kwana bisa aikin da suka yi babu gajiyawa domin taimaka ma wadanda bala'in ambaliyar ruwan ya shafa.
Mawallafiya: Halimatu Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu