Ambaliyar ruwa a Pakistan
August 4, 2010Talla
A ƙasar Pakistan ƙaruwar ambaliyar ruwa na ci gaba da haddasa asaran gidaje. Ko da yau ma mutane da yawa suka mutu, kana dubban gidaje ruwean ya rusa a arewa maso yammacin asar ta Pakistan. Ambaliyar ruwan wanda ta fara tun a makon jiya, ya hallaka aƙalla mutane 1,500, yayinda ya rusa gidaje kimanin miliyan ukku. Ma'aikatan agaji sun yi gargaɗin cewa, kogunan da suka cika a yankin na iya darewa, su tumbatsa a ko wane lokaci, inda kuma ambaliyar za ta kai har izuwa kudancin ƙasar. A yankin Punjab da ke ƙasar ta Pakistan ruwa ya share ɗaruruwan ƙauyuka, kuma yanzu haka ya fara isa man'yan birane.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu