1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ambaliyar ruwa: Dabbobi da dama sun mutu a Borno

September 11, 2024

Kashi 80 bisa 100 na dabbobin da ke gidan zoo na Sanda Kyarimi, ciki har da zakuna da kadoji da karkanda da dai sauran halittu sun mutu, yayin da wasu da dama ruwa ya yi awon gaba da su a Maiduguri da ke Najeriya.

Wata karkanda da ke gandun dajin a Afrika
Wata karkanda da ke gandun dajin a AfrikaHoto: Prabhakarmani Tewari/DW

Hukumar da ke kula da gidan ajiyar dabbobin ta fitar da sanarwar gargadi ga al'ummar birnin da su yi taka-tsantsan kasancewar wasu daga cikin dabbobin dake da hadari sun shiga cikin al'umma ciki har kuwa har da kadoji da macizai.

Karin bayani: Najeriya: Ambaliyar ruwa na ci gaba da barna

An dai samu mummunar ambaliyar ruwa sakamakon katsewar madatsar ruwan Alau da ke birnin Maiduguri, wanda hakan ya jefa dubun dubatar al'ummar yankin cikin mawuyacin hali na rasa muhallansu da kuma fargabar barkewar cututtuka har ma da asarar rayuka.

Karin bayani: Rusau sakamakon ambaliya a Maiduguri

Ambaliyar ruwan ta halaka mutane 49 a watan Agustan shekara ta 2024, a arewa maso gabashin Najeriya, yayin da a shekara ta 2022 aka samu makamanciyar ambaliyar da ta halaka mutane 600 a jwannan shiyya.