Ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Pakistan
August 5, 2022Talla
Ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama da ake ci gaba da shekawa ta yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 450 a kasar Pakistan cikin wata guda, inda galibi lamarin ya faru a yankin kusu maso yammacin kasar mai fama da talauci.
An tura hukumomin agajin gaggawa yankin gami da sojoji domin taimakon mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su.
Shi kansa Firaminista Shehbaz Sharif na kasar ta Pakistan ya kai ziyarar gani da ido inda aka samu ambaliyar ruwa sannan ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin taimakon mutanen da lamarin ya shafa.