1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iAfirka

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 188

Suleiman Babayo MAB
May 2, 2024

Hasashe ya nuna daga wannan Alhamis ruwan sama da ake shekawa babu kakkautawa zai ci gaba a Kenya da Tanzaniya da sauran kasashen gabashin Afirka, lamarin ya halaka fiye da mutane 350, wasu dubban sun rasa matsugunansu.

Ambaliyar ruwa a Kenya
Ambaliyar ruwa a KenyaHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta halaka a kasar Kenya sun kai 188 tun daga watan Maris, yayin da wasu mutanen kimanin 90 suka bace ake ci gaba da nema. A wannan Alhamis ma'aikatar cikin gida ta kasar ta tabbatar da wannan alkaluman. Akwai kuma mutane 125 da suka samu raunika. Fiye da mutane dubu-165 suka rasa gidajensu sakamakon bala'in.

Ruwan sama da ake ci gaba da shekawa babu kakkautawa, ya haifar da ambaliyar ruwa gami da zabtarewar kasa a Kenya da sauran kasashen gabashin Afirka. Tuni gwamnatin Kenya ta bai wa sojoji umurnin kwashe mutanen da suke fuskantar wannan ambaliyar ruwa.