1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gidaje da dama sun lalace sakamakon amabiyar Sudan

Suleiman Babayo AH
September 11, 2020

Fiye da mutane 100 suka halaka sakamakon ambaliyar ruwa a Sudan yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane rabin milyan ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Hochwasser im Sudan
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/M. Ali

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane rabin milyan ambaliyar ruwa ta ritsa da su a kasar Sudan, yayin da dubban gidaje suka lalace. Mahukuntan kasar sun tabbatar fiye da mutane 100 ambaliyar ta halaka sannan wasu da dama suka jikata.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jinkai ya ce akwai fargabar samun barkewar cutuka yayin da ambaliyar ruwan ta fara ja da baya. A makon jiya gwamnatin Sudan ta ayyana dokar ta baci na tsawon waatnni uku domin dakile matsalolin da ambaliyar ruwan ta haifar.