Bala'iMozambik
Mozambik cikin tasku sanadin ambaliya
January 20, 2026
Talla
Shugabar Ofishin Hukumar Bayar da Agajin Jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA a Mozambik Paola Emerson ta bayyana cewa, a yanzu kimanin sama da mutane rabin miliyan ne ke neman daukin gaggawa a kasar. Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a Mozambik da kuma makwabciyar kasa Afirka ta Kudu da aka kwashe tsawon makonni a tsugawa, ya halaka kimanin mutane 150 kamar yadda mahukuntan kasashen biyu suka tabbatar.