1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 110 a Jamus da Beljiyam

Suleiman Babayo MAB
July 16, 2021

A kasashen Jamus da Beljiyam ana ci gaba da neman mutanen da suka bace sakamakon ambaliyar ruwa wadda ta halaka mutane 110 a kasashen.

Deutschland Unwetterkatastrophe | Schuld, Landkreis Ahrweiler in Rheinland-Pfalz
Hoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

Kimanin mutane 110 suka halaka a kasashen Jamus da Beljiyam yayin da masu aikin gaggawa ke ci gaba da neman mutanen da suka makale sakamakon faruwan lamarin. Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus ke ziyarar yankin yammacin kasar wuraren  da aka samu ambaliyar ruwan, inda zai gana da ma'aikatan agajin gaggawa wadanda suke ci gaba da aikin ceton mutanen da ambaliyar ta ritsa da su. Jihohi biyu na Jamus da ambaliyar ta fi shafa su ne Rhineland-Palatinate da North Rhine-Westphalia inda mazaunin tashar DW take.

A Jamus akwai mutane 1,300 da ake ci gaba da nema bayan faruwan wannan ambaliyar. Tuni gwamnatin Jamus ta fara amfani da sojoji a aikin ceton.

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce ambaliyar ruwan na yammacin Turai ta nuna irin matsalolin da sauyin yanayi ya haifar tare da bukatar ganin an dauki mataki a kai.