Al'ummar Nijar na cigaba da kokawa dangane da halin da suka shiga bayan da wasu sassan birnin Yamai suka gamu da ambaliyar ruwan da suka sanya su barin muhallansu kana suka koma makarantu da zama. Wannan ya sanya hukumomi dage komawa makatara da aka tsara yi a farkon watan Oktoba.