1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuka a Nepal

July 7, 2024

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake tafkawa a Nepal ya haifar da samun karin ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar laka, wanda ya haifar da mutuwar mutane 14.

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuka a Nepal
Hoto: Skanda Gautam/IMAGO/ZUMA Press Wire

Kakakin rundunar 'yan sandan Nepal, Dan Bahadur Karki ya ce har yanzu ana ci gaba da neman wasu mutane tara da suka yi batan dabo a sassan kasar. A cewarsa, tawagarsa na gudanar da ayyukan ceto a yankunan da iftila'in ya shafa. Hukumar Kula da Yanayi ta kasar ta yi gargadin cewa, wasu sassan kasar za su ci gaba da fuskatar saukar ruwan sama mai karfi da kuma tsawa har zuwa gobe Litinin.

Tun a farkon watan jiya ne, iftila'in sakamakon mamakon ruwan sama da kuma walkiya ya yi sanadin rayukan mutane 50 a kasar ta Nepal.