1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iAsiya

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane biyu a Bangladesh

Suleiman Babayo ZUD
August 22, 2024

Hukumomi a kasar Bangladesh sun fuskanci kalubale kan yadda ambaliyar ruwa ta halaka mutane biyu tare da tagaiyara kimanin mutane milyan uku.

Ambaliyar a Bangladesh
Ambaliyar a BangladeshHoto: Md Shobuj

Ambaliayar ta tagaiyara kimanin mutane milyan uku a yankin gabashin kasar Bangladesh, inda hukumomi suka kaddamar da aikin ceto. Ma'aikatan aikin gaggawa sun kwashe kimanin mutane dubu-75 zuwa tudun mun tsira daga cikin kimanin mutane milyan uku da wannan ambaliyar ruwa ta tagaiyara.

Bayan kwashe kwanaki uku ana tafka ruwan sama da tumbatsar da koguna suka yi, suka haifar da wannan ambaliyar ruwan. Hukumomin kasar ta Bangladesh sun katse tafiye-tafiye jiragen kasa zuwa yankin na gabashi sakamakon bala'in da ake fuskanta.