Ambaliyar ruwan sama a Japan
July 14, 2012Talla
Hukumomi a ƙasar japan sun gargaɗhi mutane kusan dubu ɗari fuɗu da ke zaune a yankin kudu maso yammaci na ƙasar,
da su ficce daga yankin saboda ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da ake shatata wa, waɗanda tuni suka yi sanadiyar ɓatan dabo na wasu mutanen guda 29.Hukumar da ke kula da bincike sararin samaniya , ta ce a kwai yiwar an samu zabtarewar ƙasa da kuma ƙarin ambaliyar a tsibirin Kyushu ,inda aka samu centimita 11 na ruwan saman da ya faɗi a cikin awa guda.Can ma a yankin Asso da ke kan tsauni, daf da wani dutsin mai aman wuta centimita 75 na ruwan sama ya tarara ,ya yi ambaliya ya kashe kuma mutane guda 19.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala