1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ambaliyar ruwan sama ta haddasa barna

September 2, 2019

Garuruwa da dama a yankin arewa maso gabashin Najeriya ambaliyar ruwan sama ta shafe su inda ta bazama a cikin jihohi guda biyar tun daga 20 ga watan Augusta a skamakon ruwan sama da ake shekawa.

Nigeria Lokoja - Flut
Hoto: Getty Images/AFP/S. Adelakun

Mutane guda 12 suka mutu a sakamakon ambaliyar a cikin Jihohin Jigawa da Yobe da Kano da Borno. Ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya tun daga ranar 20 zuwa 25 ga watan Augusta ya yi sanadin lallata hanyoyin da gidaje kana ya tilasta wa iyalai sama da dubbu goma yin kaura. A Borno cibiyoyin 'yan gudun hijira da dama ruwan saman ya cisu inda jama'a suke cikin matsalar karancin cimmaka da ruwan sha da kuma magunguna.