1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamaru: Akwai lauje cikin nadi a rikicin Ambazoniya

September 30, 2021

Tsohon Ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Kamaru Elvis Ngolle Ngolle ya ce yunkurin dawo da zaman lumana a yankin kasar na Anglophone mai magana da turancin Ingilishi na fuskantar tarnaki.

Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Lintao Zhang

A cikin hirarsa da DW a wannan Alhamis Ngolle Ngolle ya zargi wasu mutane da bai bayyana sunayensu ba da hannu wurin dakile yunkurin sasanta rikicin domin suna amfana da abin da ake aikatawa.

Ngolle Ngolle ya yi wannan magana ne kwana guda kafin zagayowar ranar 'yancin kai da yankin Ingilishi na Kamaru ya samu daga Turawan Burtaniya tare kuma da hadewa da yankin Kamaru rainon Faransa.

Tsohon ministan da ya yi fice a cikin kasar ta Kamaru ya ce Shugaba Paul Biya na iyakar kokarinsa wurin ganin an tsagaita wuta a rikicin yankin da 'yan aware ke wa lakabi da Ambazoniya wanda a gobe Jumma'a ake cika shekaru biyar da farawa. Ngolle Ngolle ya yi gargadin cewa amfani da soji ba zai kawo karshen matsalar ba, amma kuma akwai bukatar kasashen Faransa da Jamus da Amirka da Birtaniya su shigo cikin shirin sansanta rikicin.