Amfani da hasken rana don samar da wuta a Najeriya
October 29, 2024Baya ga barazanar rashin tsaro, babban kalubalen da ke kan gaba ga arewacin Najeriya shi ne rashin wadatar wutar lantarki , inda wannan sashe ya share lokaci cikin duhu sakamakon ayyukan barayin daji. Sai dai, masu mulkin tarayyar Najeriya suka ce suna shirin sauya dabara tare komawa ya zuwa hasken rana cikin batun samar da wutar lantarkli a Arewa.
Ministan wutar lantarki na kasar Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin samar da wutar da ta kai Megawatt 100 daga hasken rana cikin jihohin yankin 19 da Abuja. Adelabu ya ce: ‘‘ Duniya na sauyawa, muna karni na 21, muna da imanin cewar tsari mafi inganci na samar da ingantacciyar wuta maras cikas a sashen arewacin tarayyar Najeriyar ita ce ta samun tsarin samar da wutar da ke zaman kansa a yankin. Tsarin kuma da a karkashinsa kowace jiha za ta samu wuta daga hasken rana."
Karin bayani: Tsadar hasken wutar lantarki a Najeriya
Kowace jiha a cikin 20 na arewacin Najeriya za ta kasance mai cin gashin kanta cikin harkar ta wutar lantarki. Kuma mun samu gaggarumin ci-gaba kan wannan, domin kuwa mun samu masu zuba jari da masu kwangilar da ke sha‘awar samar da akalla Megawatt 100 a kowace jiha da ke cikin wannan yanki. Minista Adelabu ya kara da cewa: "Za'a fara ne da Megawatt 50, kafin daga baya a kara yawan wutar zuwa Megawatt 100. In mun kai nan, za'a samu wadatuwar wuta a cikin yankin. Wannan yanki na da albarkar hasken rana, inda mafi karancin hasken ranar da kowace jiha ke samu ba ya gaza na awoyi 10 a kullum. Wannan zai rage matsin da ke kan layin samar da wutar tarayyar Najeriyar, sannan zai wadatar da wuta a daukacin kasar.’’
Yawan kudin da za a kashe don samar da wuta
Tun kafin matsalar barayin dajin cikin batun na wutar lantarki, arewacin tarayyar Najeriyar na zaman na baya ga dangi cikin batun wutar, inda kamfanoni da yawa suka rufe sakamakon rashin wutar sarrafa kayan da ke cikin masana’antun. Sai dai, a yayin da masu mulkin suke da sabon fata a batun wuta, kalubalen da ke gabansu na zaman kashe kudin maras adadi a kokari na kaiwa ga butar dake da tasiri ga tattali na arziki da siyasa.
Karin bayani: An kara kudin wutar lantarki a Najeriya
Ana da bukatar akalla dalar Amurka miliyan dubu biyu kan hanyar cika burin da ke iya tayar a kamfanoni da samun aiki a tsakanin miliyoyin matasan yankin, lamarin da ke bukatar karin Megawatt 2000. Ko da Ibrahim Sani, da ke zaman kwarare a harkar wuta ta hasken rana, sai da ya ce wannan tsari na iya sauya batun wutar lantarki a daukacin arewacin tarayyar Najeriya.
Ya sabon tsarin rabon wuta zai kasance a Arewa?
Babban kalubalen da ke gaban wutar da ke zuwa arewacin kasar na zaman hadewarta a karkashin tsari na dogaro da juna. Daukacin jihohin arewacin Najeriya na dogaro ne da hanyar rabon wutar guda biyu. Sai dai, abun da ke faruwa cikin arewacin kasar a halin yanzu, a fadar Usman Guru Mohammed, da ke zaman tsohon shugaban kamfanin rabon wutar kasar TCN bai rasa nasaba da hadewar tsarin rabon wutar lantarki wuri guda.
Karin bayani: Zanga-zangar kan dauke wutar lantarki
Batun rashin wutar lantarki na zaman na kan gaba a cikin jerin matsalolin da ke barazana ga kokarin tarayyar Najeriya na kaiwa ya zuwa girman tattalin arziki da kauce wa annobar rashin tsaron da ke ta karuwa cikin kasar.