Kwango: Amfani da salula na dakile tsaro
July 16, 2026
Rundunar sojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon na zargin cewa, dabi'ar mu'amala da wayoyin salula da sojojin ke yi na zama babbar barazana ga tsaron lafiyarsu. Bugu da kari rundunar sojojin ta Kwango ta ce, amfani da wayoyin na taimakawa rashin samun nasarar da sojojin kasar ke yi a fafatawa da abokan gabarsu musamman a yankin Gabashin kasar. Shekaru da dama kenan dai da ake yawan cin karo da dimbin bidiyoyin da ke nuna sojojin gwamnatin kasar Kwangon ko mayakan sa-kai na Wazalendo a shafukan sada zumunta, suna daukar kansu da kansu.
Fargabar tsaro, ko hana aika sako?
Sau da dama a ciki suna nuna ko dai nasarorin da suke samu a fagen daga, ko suna yin kiran neman dauki. A wasu bidiyoyin sojojin na korafin fama da suke da rashin kayan yaki da kudi, ko kuma suna arcewa daga fagen dagar. A wata sanarwa da ya fitar kakakin rundunar sojojin kasar ta Kwango Laftanal-Kanal Mak Hazukay ya bayyana wa sojojin kasar cewa, hasken wayar salula na iya bayyana wurin da wasu sojojin suke. A cewarsa, hakan ka iya taimaka wa abokan gaba saurin tantance maboyar sojojin su iya bude musu wuta a cikin sauki.
A kan haka ne ya gargadi sojojin kasar da su kauracewa amfani da wayar salula ba tare da izini ba, sannan su daina yada bididoyi wadanda ke nuna wajen da suke ko suka dosa a tafiyarsu ko yawansu ko kuma suke fafatawa a shafukan sada zumunta na zamani. Kelvin Bwija wani dan fafutuka a yankin Uvira na kasar ta Kwango ya bayyana goyon bayansa ga matakin rundunar sojin kasar wanda ya ce, zai taimaka a rage yawan cin amanar da ake fuskanta a tsakanin sojojin.
Bukatar amfani da shawarar shugabannin
Maître Aimé Bisimwa wani dan kungiyar kare hakin dan Adam a Kwangon cewa ya yi, ya kamata sojoji su yi biyayya ga umurnin shugabanninsu duk da yake a wannan zamani wayar salula na da matukar muhimmanci wajen biyan wasu bukatu na jama'a. Yanzu haka dai a fagen dagar ana ci ga da gwabza fada a tsaunikan kauyikan Mwenga da Fizi na yankin kudancin Kivu tsakanin kawancen rundunar sojojin kasar ta Kwango da kungiyar 'yan sa-kai ta Wazalendo da makayan kawancen kungiyar tawayen M23 da kungiyar Twirwaneho, wadanda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nunar suna samun goyon bayan Ruwanda.
Fassara: Gazali Abdou Tasawa
Gyarwa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar