1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Amina: Sarauniyar Zazzau

Pinado Waba LMJ/MNA
August 26, 2021

A lokacin da maza suka mamaye harkokin rayuwa, aka samu Sarauniya Amina ta Zazzau. Gwarzuwa Bahaushiya, wadda ta jagoranci yaki domin fadada daula.

DW African Roots | Queen Amina of Zazzau

Ya za a takaita abin da sarauniyar Zazzau Amina take kai?

Sarauniya Amina, mace mai kamar maza!' Wannan shi ne kirarin da ake yi mata. Duk abin da ta yi a matsayin sarauniya ya zarta wadanda takwarorinta maza suka yi. A yanzu tana wakiltar jarumta da jajircewar mata.

Yaushe kuma a ina Sarauniya Amina ta rayu?

An yi amannar cewa an haifi Sarauniya Amina a karni na 16, sai dai ra'ayoyin masana  sun banamta kan takamaiman ranar haihuwarta. Ta rayu a inda yanzu ya kasance birnin Zariya da ke jihar Kaduna a Najeriya.

Da me ake tuna Sarauniya Amina?

  • An fi tuna ta a matsayin shararriyar gwarzuwa
  • Ta yi mulki na tsawon shekaru 34, ta kuma fadada masarautarta ta hanyar kame wasu garuruwan. Ta kuma bude hanyoyin kasuwanci, an kuma yi amannar cewa ita ta assasa noman goro a yankunan da ta mulka.
  • Sultan din Sokoto na biyu Mohammed Bello da ya ksance da ga fitaccen malamin nan da ya yi jihadin Musulumci Shehu Usman dan Fodio ne ya fara rubutu a kanta cikin littafinsa na 'Infaku'l Maisuri. Ya bayyana cikin littafin nasa cewa Sarauniya Amina ce ta fara kaddamar da tsarin gwamnati a kasar Hausa kuma tana da baiwar shugabanci ta musamman.

Wacce takaddama ake fama da ita kan rayuwar sarauniya Amina?

  • Wasu na ganin labarin Sarauniya Amina almara ce kawai ba ta taba rayuwa ba. Sai dai akwai shaidu da ke nuna ta rayun. Misali guda shi ne ganuwar da ta giggina a kewayen biranen da ta kame. Haka kuma har yanzu akwai wasu gine-gine da alammomi na inda ya kasance fadarta da inda take bai wa mayakanta horo a Zariya.
  • Amina: Sarauniyar Zazzau

    02:03

    This browser does not support the video element.

  • Duk da yake ba ta haihu ba, akwai zargin cewa wasu daga cikin tsatson 'yan uwanta na jini na cikin shugabannin da ke da mukamai a masarautar.
  • Har yanzu akwai tababa kan dalili da kuma inda ta rasu, abin da aka fi yadda da shi shi ne ta rasu a fagen daga a garin Atagara da a yanzu yake cikin jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Ya ake tuna Sarauniya Amina a Najeriya ta yanzu da wasu wuraren?

  • Wurare da dama a cibiyoyi da hukumomin gwamnati a arewacin Najeriya na dauke da sunanta. Guda daga cikinsu shi ne makarantar sakandaren gwamnati ta Queen Amina College da ke jihar Kaduna. Akwai dakunan kwanan dalibai mata a jami'ar Ahmadu Bello da ke zariya da jami'r Lagos da ake kira da Queen Amina Hall.
  • An yi hasashen cewa jarumar wasan kwaikwayon "Warrior Princess" da ake yadawa a gidan talabijin din Amirka 'Xena, na kwaikwayon Sarauniyar Zazzau Amina.

Wadanda suka taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hada da Farfesa Doulaye Konaté masanin tarihi da Dr Lily Mafela, gami da Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.