1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta amince da kudiri kan yankunan Ukraine

Binta Aliyu Zurmi ATB
October 4, 2022

Majalisar dattawan Rasha, ta amince da kudirin shigar da yankunan Ukraine hudu da gwamnatin Shugaba Putin ta ayyana cikin kasarta a hukumance wadanda suka hada da Donetsk da Luhansk da Kherson da kuma Zaporizhzhia.

Hoto: Federation Council/AP Photo/picture alliance

Da gagarumin rinjaye majalisar dattawan kasar Rasha ta kada kuri'ar amincewa da yankunan hudu da aka gudanar da zaben raba gardama domin shigar da su a cikin kasar a hukumance. A makon da ya gabata gwamnatin Rasha ta kaddamar da wakilian a yankunan Donetsk da Lougansk da Zaporizhzhia da Kherson da ta mamaye a Ukraine. 

Da take jawabi bayan kammalla kidayar kuri'un da 'yan majalisun suka kada, shugabar majalisar dattijai Valentina Matviyenko ta jinjina wa takwarorinta bisa wannan mataki da suka dauka, inda ta kara da cewa.

"Ina da tabbacin dukkanimu mun san girman nauyin da ke kanmu, sauke wannan nauyi na wakilcin al'ummarmu ba abu ne da ke da sauki ba amma na tabbata wannan rana ta yau za ta zama mai cike da tarihi bisa wannan mataki da muka dauka"

Rasha | Shugabar majalisar dattijai - Valentina MatviyenkoHoto: Alexander Demianchuk/TASS/dpa

Sai dai duk da wannan, su ma a nasu bangaren mahukunta a Ukraine na ci gaba da samu nasara a yayin da suka fatattakar sojojin Rasha daga yankin Lyman. Kakakin gwamnatin Rasha Dimitri Peskov ya ce tun da farko sun bayyana wa dunyia matsayarsu, abin da ya rage shi ne daga bangaren Ukraine su san me ya kamata su yi.

"A lokacin sulhu ana bukatar bangarori biyu domin tattaunawa, a namu bangaren, kowa ya san me muke so tun ma kafin sojojinmu su shiga yankunan Ukraine, kuma mun yi duk iya yinmu na magance matsalar ta hanyar diplomasiyya amma abin ya faskara, yanzu za mu jira mu ga ko shugban na Ukraine zai canza matsayarsa ko kuma wani shugaba da kasar za ta yi a nan gaba ya sauya tunani domin al'ummar kasar"

Mutane a Moscow na murnar shigar da yankunan Ukraine hudu cikin RashaHoto: Alexander Shcherbak/dpa/TASS/picture alliance

Sojojin Ukraine sun nuna garuruwan da suka kwace daga hannun dakarun na Rasha, abin da ke nuna shugaban na Rasha zai fuskanci karin matsin lamba daga cikin gida, saboda irin yadda lamura ke sukurkucewa kasar kan yadda yakin ke tafiya.

Kasashen yammacin duniya da dama sun yi Allah wadai da matakin Rasha na hade yankunan a matsayin nata, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kakkausar suka kan matakin tare da bayyana shi a matsayin wanda bai da gurbi a wannan zamani. 

Ukraine ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar da ya yi wani zaman gaggawa don duba batun.