Amincewar Iran da Shawarar Hukumar IAEA
November 3, 2009Daulolin ƙasashe masu ƙarfin tatalin arzikin masna´antu sun sake yin kira ga ƙasar Iran, da ta amince da sharuɗɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya mata kan shirin ta na makamashin nukliya.
Wannan matsin lambar ta zo ne a yayin da ƙasar Iran tace ta amince da sayan makamashin nukliya kai tsaye daga ƙasashen yamma a mai makon aikawa da sinadarin Uranium zuwa ƙasashen na yamma domin bunƙasa shi . Mahunkunta a birnin Moscow na ƙasar Rasha waɗanda ke ƙawance na ƙut da ƙut da ƙasar Iran sun buƙaci Iran da ta amince da wannan tayi da Majalisar Ɗinkin Duniya tayi mata akan shirinta na nukliya wanda ake ta taƙardama a kai .
Ƙasar Iran a yanzu haka ta shiga wani hali na tsaka mai wuya a cewar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, wadda a ganin ta amincewar ƙasar Iran da wannan tayi zai nuna cewar Iran ba zata so a mayar da ita saniyar ware ba, kuma a shirye take da ta ba da haɗin kai akan manufa. Shugaban hukumar kula da makamashin nukliya ta duniya Mohammed El-Baradai tuni yayi kira ga ƙasar Iran game da mayar da martanin gaggawa kan tayinsa kuma yayi kira ga sauran ƙasashe da su ba da haɗin kai don samun ci gaba. A nasa ɓangaren ministan harkokin wajen ƙasar Iran Manouchehr Mottaki kira yayi da a sake yi wa tayin kwaskwarima a lokacin da yake ziyarar ƙasar Malasia. Yace kwanaki biyu da suka gabata mun miƙa shawarwarinmu ga hukumar kula da makamashin nukliya ta duniya wanda kuma na yi amannar cewar hakan zai sa a kafa cibiyar da zata mayar da hankali kan buƙatunmu sa´anan tayi duk kwaskwariman da ya dace.
Wakili na musamman da Iran ta tura zuwa hukumar kula da makamashin nukliyar ta duniya Ali Asghar Soltanieh, a cikin bayaninsa a birnin Vienna yace a shirye Iran take da ta sai makamashi a ko'ina duk faɗin duniya a ƙarƙashin kulawar hukumar IAEA kamar yadda ta saya daga ƙasar Argentina shekaru ishirin da suka shige.
A ɓangaren ƙasar Faransa kuwa ministan harkokin wajen ta Bernard Kouchner cewa yayi manyan dauloli ƙasashen duniya guda shida da suke tattaunawa da ƙasar Iran kan shirin makamashin nukliyanta ba zasu amince da jinkirin na Iran ba.
Ƙasahen yankin Gulf kuwa a yanzu haka sun zura ido don ganin yadda abubuwa zasu kaya domin kuwa sune na kurkusa da duk wani mataki da Iran zata ɗauka zai shafesu.
Mawallafi: Rahmatu Abubakar Mahmud
Edita: Ahmad Tijani Lawal