Martanin Amirka bayan marabus din Saad al-Hariri
October 30, 2019Talla
A cikin wata sanarwa da sakataran harkokin wajen Amirkan Mike Pompeo ya bayyana ya bukaci 'yan siyasar na Libanon da su nuna dattako. Marabus din dai na firaminsta Libanon zai kara saka kasar cikin wani hali na rashin tabbas watanni takwas da kafa gwamnatin wacce aka kwashe dogon lokaci ana tattaunawa kafin kafuwarta.
jama'ar na Libanon sun share kusan makonni biyu suna yin zanga- zanga domin ganin firaministan ya yi marabus, sakamakon gaza magance tarin matsalolin da kasar take fama da su na cin hanci da talauci da kuma matsalolin tattalin arziki.