Amirka: Blinken ya fara ziyara a Afirka
November 17, 2021Talla
Blinken zai kuma tattauna kan batun sauyin yanayi da rikicin kasashen Habasha da Sudan da kuma yadda za a inganta samar da allurara rigakafin annobar corona a nahiyar, lamarin da ke kasancewa fatan shugaba Biden na kerewa kasar China da ke tabbatar da ingancin nata.
Baya ga kasar Kenya da ya isa, ana sa ran daga bisa zai je Najeriya da ke zama kasa mafi yawan al'umma a nahiyar da kuma kasar Senegal. Blinken dai na kokarin nuna bambancin gwamnatin kasar a yanzu da ta tsohun shugaban kasar Amirka Donald Trump wanda ke zama shugaba daya tilo cikin shekaru da bai kai ziyara nahiyar ba, ya kuma tozarta bakin haurenta.