1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ce kan gaba wajen sayar da makamai

Ahmed Salisu
March 11, 2019

Cibiyar SIPRI da ke bincike kan zaman lafiya da yaduwar makaman nukiliya ta ce Amirka ce ke kan gaba wajen sayar da makamai a 2018.

Panzer-Geschäft - Leopard 2 A7+
Hoto: picture-alliance/dpa

A rahoton da cibiyar ta SIPRI ta wallafa ya nuna cewa kasar Amirka ce ke kan gaba wajen sayar da makamai ga kasashen duniya inda ta sayar da fiye da kashi daya cikin uku na makaman da ta ke kerawa. Kazalika cibiyar ta sanar da cewa kasuwar makaman ta haura da kashi 8% cikin 100 tsakanin shakurun 2014 zuwa 2018 idan aka kwatanta da shekarun 2009 zuwa 2013.

Jiragen yaki na daga cikin makaman da Amirka ke sayarwaHoto: picture-alliance/dpa/J. Heon-Kyun

Rahoton na SIPRI ya kuma ce kasar ta Amirka ta samar wa kasashe kusan 100 da makamai daban-daban da suka hada da jiragen yaki da makamai masu linzami da ke cin gajere da dogon zongo da kuma dimbun bama-bamai masu amfani da kimiyar wannan karni. A cewar Aude Fleurant mai kula da sashen binciken saye da sayar da makamai ta cibiyar ta SIPRI, Amirkar ta sayar da rabin makaman da ta ke kerawa ne a yanki gabas ta tsakiya inda kasar Saudiya ke kan gaba wajen sayen makaman.

Baya ga Amirka, kasashen Burtaniya da Faransa na daga cikin masu samar da makamani a yanki na gabas ta tsakiya inda bukatar kayan yaki ta ninka a shekarun 2014 zuwa 2018. Cibiyar ta SIPRI ta ce makamai kirar Amirka da Burtaniya da Faransa ne aka fi bukata a yankin Gulf inda rikice-rikice da yakin basasa suka zama ruwan dare gama duniya kuma kasashen Masar da Dubai da kuma Iraki ne a sahun gaba wajen sayen makaman.

Najeriya na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen sayan makamai a AfirkaHoto: DW/Katrin Gänsler

Rahoton na ya kuma ce kasar Rasha ita ke a matsayin kasa ta 2 a sayar da makaman domin ta na sayar da makamai ga kasashe 48 wanda suka hada da Indiya da China da Vietnam. Da cibiyar ta SIPRI za yi tsokaci kan nahiyar Afirka kuwa, jami'ar cibiyar Aude Fleurant ta ce kasashen Afrika da ke kudu da Sahara da suka fi sayen makamai sun hada da Nigeria da Angola da Sudan da Kamaru dakuma Senegal. A jimilce wadanan kasashe 5 na sayen kashi 57% cikin 100 na makaman da ke shiga wannan yanki.