Amirka: Ci gaba da barazanar kai hari Siriya
April 11, 2018Talla
A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, Shugaba Trump na Amirka ya zargi kasar Rasha da ke zaman babbar mai marawa gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriya baya, da laifin kai harin makami mai guba kan 'yan tawaye a birnin Douma na yankin gabashin Ghouta, zargin da Rasha da siriya suka sha musantawa.
Rasha dai ta sha alwashin kakkabo duk wani makami mai linzami da za a harba kasar ta Siriya. Sai dai kuma shugaban Amirka ya ce Rashan ta shirya, domin kuwa makami mai linzami sabo fil na nan tafe. Daga nata bangare kasar Turkiya da ke da ruwa da tsaki akan rikicin na Siriya, ta yi kira ga kasashen na Rasha da Amirka da su daina wannan fada da suke da ke zaman fadan kan titi.