Amirka da EU za su gana kan Siriya
March 9, 2016Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da takwarorinsa daga kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya za su gana a ranar Lahadi idan Allah ya kaimu a birnin Paris na kasar Faransa domin tattaunawa kan rikicin Siriya gabannin tattaunawar zaman lafiya da za a yi a Geneva.
Jami'an diflomasiyar guda biyar za su tattauna domin jin ina aka kwana game da batun tsagaita bude wuta da ya fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabarairu Jean-Marc Ayrault a yayin ziyararsa ta kwanaki biyu a birnin Alkahiran Masar, ya bayyana cewa idan har ana samun ci gaba za su yi duk abin da ya dace na ganin bangaren 'yan adawa ya koma cikin tattaunawar.
Har ila yau Ayrault ya ce ministocin harkokin waje daga kasashen Turai za su tuntubi Amirka da Rasha su cigaba da yin nazari kan mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wutar a Siriya bisa fatansu na ganin hare-haren Rasha ya tsaya ne kan 'yan ta'addar IS da Al-Nusra ba wai masu sassaucin ra'ayi ba.