1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Iran sun yi musayar fursunoni

Ahmed Salisu
December 7, 2019

Mutumin nan dan Amirka da ake tsare da shi a Iran tun cikin shekarar 2016 bisa zarginsa da lekan asiri ya samu fita daga gidan yarin Evin da ke Tehran, babban birnin kasar ta Iran.

Bildkombo - Trump und Rohani

A wannan Asabar din ce aka saki mutumin mai suna Xiyue Wang bayan da Amirka da Iran din suka amince kan su yi musayarsa da wani masanin kimiyya dan kasar ta Iran mai suna Massaud Soleimani da Amirka ke tsare da shi.

Ministan na harkokin wajen Iran din Mohammad Javad Zarif ne bayyana batun wannan musaya da bangarorin biyu suka amince da ita a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya jinjinawa wanda ya ce sun taka rawa kan hakan ciki kuwa har da kasar Switzerland.

Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban Amirka Donald Trump ya ce mutumin da iran din ta saki ya kama hanyarsa ta komawa gida domin saduwa da iyalansa.