Amirka da Taliban sun yi musayar fursunoni
June 1, 2014Talla
Wannan musayar fursononin tsakanin mayakan Taliban da gwamnatin Amirka, kasar Qatar ce ta jagoranci aka yi shi. Kungiyar Taliban a Afganistan ta saki wani sojan Amirka da ta kama shekaru biyar da suka gabata, yayin da ita kuwa Amirka ta saki wasu 'yan Taliban biyar da suke tsare a gidan yarin Guantanamo. Sojan na Amirka da aka sako Sergeant Bowe Bergdahl, a yanzu haka an kawo shi kasar Jamus domin duba lafiyarsa, a wani sansanin sojojin Amirka da ke kasar ta Jamus.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasir Awal