1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da hari kan 'yan IS a Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2021

A wani mataki na mayar da martani kan mayakan IS da suka dauki alhakin kai harin da ya hallaka dimbin jama'a a birnin Kabul na Afghanistan, rundunar tsaron Amirka ta kai hari kan mayakan IS da jirgi maras matuki.

Afghanistan | Kabul Airport Explosion
Hoto: REUTERS

Rundunar tsaron Amirka ta kaddamar da wani hari da jirgi maras matuki kan mayakan IS K a Afghanistan, inda tace ta halakka wadanda suka kaddamar da harin filin jirgin Kabul da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da sojojinta 13.

A share daya kuma ma'aikatar jakadancin Amirka a Afghanistan ta yi kira ga 'yan kasarta da su gaggauta kauracewa filin jirgin saman Kabul bisa fargabar barazanar kaddamar da wani mummunan harin ta'addanci.

Maimagana da yawun fadar gwamnatin Amirka Jen Saki, ya bayyana a yayin wani taron manema labaru da cewa kwanakin da ke tafe na kasancewa mafi muni, a daidai lokacin da wa'adin kwanaki na kwashe masu neman barin Afghanistan din ke kara karatowa.

Ko a yammacin jiya ma dai Amirka ta karyata kama iko da wasu sassan hilin sauka da tashin jiragen birnin Kabul da Kungiyar Taliban ta ce ta yi, tana mai cewa shaci fadi ne kawai.