1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hotunan kisan Abu bakr al-Baghdadi,

Abdourahamane Hassane
October 31, 2019

Fadar Pentagone ta Amrika ta bayyana hotunan bidiyo na farko na hare-haren da sojojinta suka kai a Siriya wanda suka kai ga halaka Abu Bakr al-Baghdadi jagoran IS.

Daya daga cikin hotunan bidiyon da Amirka ta saki
Daya daga cikin hotunan bidiyon da Amirka ta sakiHoto: picture-alliance/AP/US Department of Defense

Fadar ta Pentagone din ta bayyana hotunan ne a lokacin wani taron manema labarai inda aka rika nuna yadda wasu sojojin Amirka suka kai hari a kauyen da Abu Bakr al-Baghdadi ya buya a arewa ma so yammacin Siriya. A karin hasken da fadar ta bayer ta ce al-Baghdadi ya tayar da bam din da ke a jikinsa a karkashin ramin da yake boye wacce ta kasheshi tare da wasu yaran. Sai dai fadar ta Pentagone ta ce sojojin Amirka sun yi kokarin kare wasu yaran tare da kama wasu mutane guda biyu da ke dauke da wasu na'urori.