Ana cigaba da zanga-zanga a Amirka
May 31, 2020Talla
Lauya Ben Crump ya kara da cewar yana da tabbacin za a samu shaidun da zasu tabbatar da cewar 'dan sandan Derek Chauvin mai shekaru 44 ya gudanar da wannan mummunar aika-aika ne da gangan.
Binciken da likitoci suka gudanar kan gawar George Floyd ya nunar da cewar daga cikin abubuwan da suka yi sanadiyyar mutuwarsa akwai shakar da 'Dan sandan ya yi masa da lalurar ciwon zuciya da ya ke fama da ita da kuma alamun barasa a jikinsa. Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye rubuce da kalmommin marigayi Floyd na karshe watau ''na kasa numfashi''.