1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antony Blinken ya isa a birnn Doha

Abdourahamane Hassane
June 12, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa a birnin Doha na Qatar da nufin warware rikicin Isra'ila da Hamas

Hoto: Ibraheem Al Omari/AP/picture alliance

 Blinken ya kuduri aniyar ganin an tsagaita bude wuta a Gaza, yana mai bayyana fatan ganin an dinke bambance-bambancen da ke tsakanin Hamas da Isra'ila bayan shafe watanni takwas ana yaki. Kawo yanzu a halin da ake ciki a fagen dagga Isra'ila na ci gaba da kai wa sassa da dama na yankin Falasdinawa da ta yi wa kawanya hare-hare. Hamas ta sanar da cewar ta mika wa masu shiga tsakani na Qatar da Masar martaninta kan shirin da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar a ranar 31 ga watan Mayu, wanda ya tanadi tsagaita wuta, da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da  Isra'ila. Sai dai ba a bayyana abin da ke cikin martanin ba.