1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na fuskantar matsin lamba

November 19, 2022

Amirka na matsa lamba ga kasar Ukraine kan ta zauna kan teburin tattaunawar zaman lafiya da Rasha, bayan da Pentagon ta ce akwai bukatar kasashen biyu su yi zaman sulhu.

Hafsan hafsoshin sojan Amurka Janar Mark Milley
Hoto: Semansky Patrick/abaca/picture alliance

Matsin lambar dai na zuwa ne bayan da wani babban jami'in hukumar tsaron Amirka ta Pentagon ya ce, da kamar wuya gwamnatin Kyiv ta iya sake kwace ikon dukkanin yankunan kasarta da ke karkashin ikon Rasha.

Hafsan hafsoshin sojan Amurka Janar Mark Milley, ya sake jadadda goyon bayan da Amirka da kuma kawayenta ke bai wa Ukraine, sai dai ya kara da cewa nasarar da Kyiv take samu a yanzu ne ya nuna bukatar ta fara tattauna da Moscow.

Sai dai a ranar Juma'a, kakakin fadar White House ya bayyana cewa Amirka bata kokarin tilastawa Ukraine ta zauna kan teburin sulhu ko kuma ta ba da kai bori ya hau.

A farkon watan Nuwambar nan da muke ciki ne dai shugaban na Ukraine ya yi watsi da sharaddinshi da ke cewa, har sai shugaba Putin ya sauka daga kan mulki zai amince da tattaunawar zaman lafiya.