Amirka na sa ido a kasashe da ake da Ebola
October 26, 2014Talla
Masu aiko da rahotanni suka ce jakaddiyar za ta yi amfani da wannan ziyarar don tantance irin gibin da ake da shi a yakin da kasashen duniya ke yi da wannan annoba wadda ta yi sanadin rasuwar mutanen da dama.
Uwargida Samantha ta ce bayan kammala zaiyararta a Gini za kuma ta je Saliyo da Liberiya inda nan ma cutar ta yi ta'adin gaske don ganewa idonta, daga bisani kuma ta shaidawa shugaban Amirkan Barack Obama irin abinda ta gani don sanin matakin da zasu dauka tare da sauran kasashen duniya da suka daura damarar yaki da cutar.
Ebola dai inji Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi sanadin rasuwar mutanen da suka tasamma dubu biyar yayin da wasu kimanin dubu goma yanzu haka ke dauke da ita kuma ake fargabar da dama daga cikin na iya rasuwa.