1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Amirka da EU na da sabanin ra'ayi a kan Nijar

October 26, 2023

An samu rarrabuwar kawuna tsakanin kungiyar Tarattayar Turai EU da kuma Amirka kan gwamnatin mulkin sojin Nijar.

Hoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

A yayin da EU ke duba yiwuwar kakaba wa sojojin Nijasr takunkumi, ita kuwa Amurka ta na ci gaba da dasawa da gwamnatin na soji. Ministocin harkokin waje na kasashen EU 27 sun amince da wani kuduri da ka iya lafta wa Nijar takunkumai. A cewar wata wasikar da kungiyar ta fitar, za a kakaba takunkuman ne kan mutane da kuma kungiyoyin da suka yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye.Wannan dai alama ce da ke nuna EU za ta bi sahun kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS wajen hana jagororin mulkin sojin Nijar din numfasawa.

Rarrabuwar kawuna tsakanin Amirka da EU a kan Nijar

Hoto: Télé Sahel/AFP

Tun da farko dai Tarayyar Turai din ta yi Allah wadai da juyin mulkin na Nijar kamar yadda babban jami'in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Joseph Borrel ya bayyana. Borrel ya ce wannan matakin ya na nuna karfin goyon bayan EU ga ECOWAS da kuma kakkusar suka kan juyin Mulki. To sai dai kuma a daya bangaren Amirka ta sanar za ta ci gaba da dasawa da masu ruwa da tsaki kan juyin mulkin, lamari da ke nuna banbancin ra’ayi tsakanin Amurkawa da ‘yan kasashen EU wajen neman warware rikicin na Nijar.Tun bayan juyin mulkin dai Beljiyam ta yanke shawarar daina dankawa Nijar tallafin da take bata da kuma dakatar da ayyukan tsaro.Kag Sanusi wani mai sharhi ne kan al’amuran siyasa, ya kuma nuna shakku kan yiwuwar tasirin takunkumai kan Nijar a yanzu.
Ya ce “ babu wani mataki da zai saka gwamnatin da ke ci ta sauya matsaya. Takunkuman ECOWAS su ne mafi muni, amma duk da haka a yau Nijar ta na kan kafafunta duk da kalubale da take fuskanta. Bana tunani takunkumai sa su sanya kasa sauya manufofinta, abune da ake iya zama kan shi a tattauna”.

Amirka na son ci gaba da yin hulsda sda Nijar

Hoto: AP

Shi kuma masanin harkokin tsaro da siyasa Seidik Abba ya ce matakin takunkumai daga EU na nuna cewa sannu a hankali hakurinta ya fara karewa ne. Ya ce “saura kwanaki kadan sojojin su cika watanni uku da yin juyin mulki, sannan babu haske kan mayar da mulkin hannun farar hula a Nijar. Ban yi mamakin haka ba, ina ganin bayan karewar hakurin EU wannan matakin na takunkumi za ta sanya shi ne domin matsin lamba ga mayarda Nijar kan tafarkin dimokradiyya. Ita kuma Amurka a nata bangaren, ta na nuna bukatar tattaunawa ne da sasanci bayan ta dakatar da tallafi da take bai wa Nijar bayan juyin mulkin.