Yunkurin sasanta rikicin Yemen
September 27, 2021A karon farko tun bayan zama shugaban kasar Amirka, Shugaba Joe Biden ya tura Jake Sullivan, Sakataren harkokin tsaron kasar zuwa Saudiyya don ganawa da Yarima Mohammed bin Salman a game da rikicin kasar Yemen. Amirka na son ganin Saudiya ta tsagaita bude wuta a fadan da take da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.
Sullivan zai kai wannan ziyarar a wannan Litinin, a daidai lokacin da rikicin na Yemen da aka kwashe fiye da shekaru shida, ke kara tsananta. Sama da rabin al'ummar kasar na fuskantar barazanar yunwa a yayin da yara da dama ke fama da cututtuka ba tare da samun magani ba.
Amirka dai, na ganin akwai yiyuwar dakatar da fadan ba tare da Shugaba Biden ya gana gaba da gaba da Yeriman Saudiyyan ba, ana kuma cike da fatan cewa, wannan ziyarar za ta yi tasiri a janyo bangarorin da ke jayayya da juna, wajen amincewa da tsagaita bude wuta tare da hawa kan teburin sulhunta rikicin da ya janyo asarar dubban rayuka.