Amirka ta amince da bai wa Ukraine tallafin yaki
April 21, 2024Talla
Majalisar wakilai ta Amirka ta bayar da tallafin dala biliyan 95 ga kasashen ketare a kuri'ar da aka kada wanda ba a saba ganin irinsa ba na samu goyon bayan bangarori biyu.
Babban kunshi tallafin shi ne na dala biliyan 61 da za a bai wa Ukraine wanda ya hada da makamai da za ta ci gaba da yakar Rasha. Isra'ila za ta samu kason dala biliyan 13 yayin da aka ware dala biliyan 9 a matsayin tallafi ga Zirin Gaza.
A yanzu za a mika bukatar kunshin tallafin da aka dauki watanni ana kai ruwa rana zuwa gaban majalisar dattawa domin ta aminci kafin ya isa gaban Shugaban kasar Joe Biden, wanda tun a shekarar da ta gabata yake kira ga 'yan majalisar da su mika bukatar.