Amirka za ta haramta shigar da mai daga Rasha
March 10, 2022A wani mataki na ladabtar da Rasha bisa kutsen da take ci gaba da yi a makwabciyar kasar watau Ukraine. Majalisar wakilan Amirka ta amince da kudirin doka da za haramta shigar da mai daga kasar Rasha da ma sauran wasu makamashi a kasar.
Kazalika za a yi nazari a kan matsayin Rasha a kungiyar kasuwanci ta duniya watau WTO, matakin da zai janyo karin wasu takumkumai akan wasu manyan jami'an gwamnatin Rashar da ake zargi da take hakkin bil-Adama.
'Yan majalisun Amirkan kama daga jam'iyyar adawa da ma ta mulki sun kosa su dauki mataki duk kuwa da halin matsi da ma karuwar farashin makamashi daga Rashar zai haifar a kasar.
Yanzu za a mika wa majalisar dattijaai domin daukar nata matakin kafin shugaban kasa ya kai ga sa hannu ta zama cikakkiyar doka.
Kasashen yamma dai na ci gaba da kakaba wa Rasha takunkumai tun bayan da ta yi watsi da duk wasu hanyoyin yin sulhu ta hanyar diflomasiyya.