1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta samu bama-baman da za ta fasa mabuyar Hamas

December 2, 2023

Rahotanni sun nuna yadda sararin samaniyar Zirin Gaza ya turnuke da hayaki na hare-haren Isra'ila yayin da Amirka ke kokarin kai wa Isra'ila wadannan bama-bamai.

Hoto: Avi Ohayon/Israel GpoI/Zuma/MAGO

Amirka ta bai wa Isra'ila tallafin manya-manyan bama-bamai da ke da karfin fasa ramukan karkashin kasa a yankin Zirin Gaza, inda kungiyar Hamas ke yaki da makamai. Mujallar Wall Street Journal ce ta fitar da wannan labari da ta ce Amirka ta fara mika wa Isra'ila wadannan bama-bamai tun kafin barkewar sabon yaki a watan Oktoban da ya gabata.

Mujallar ta ce bama-bamai 100 da sauran wasu makamai sama da 70,000 ne Amirka ta bai wa Isra'ila domin yakar kungiyar Hamas da ke labewa a cikin ramukan karkashin kasa a yankin Zirin Gaza.

Wannan na zuwa ne a yayin da aka shiga rana ta biyu da dakarun Isra'ila suka ci gaba da barin wuta a Gaza tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda. Ma'aikatan kiwon lafiya a wani asibitin Gaza sun ce kusan mutum 200 ne aka halaka tun bayan dawo da ci gaba da hare-hare a baya-bayan nan.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani