Amirka ta bukaci Iran ta bada hadin kai ga AEIA
March 6, 2013 Kasar Amirka ta bukaci da hukumomin kasar Iran da su bada hadin kai ga hukumar makamashi ta kasa da ksa domin binciken wasu tashoshinta na nukiliya . Wakilin Amurka a hukumar makamashin ta AIEA Joseph Macmanus,yace duniya fa ta gaji da kallon kasar Iran na daukar kai ga maganar nukiliyarta, don haka lokaci yayi inda ya kamata a yita a kare da kasar don kowa ya kama gabansa.
Bayan shekaru kusan goma ana taci bata ci ba da kasar ta Iran a dangane da shirinta na nukiliya, kawo yanzu dai hukumar ta makamashi ta kasa da kasa bata tantance manufar kasar ta Iran ba a dangane da batun, shirin da hukumomin na Iran suka jajirce cewar na samar da makamashi ne domin aikin farar hulla hujjar da kasashen duniya suka yi watsi da ita suna zargin kasar da shirya makaman kare dangi.
Kawo yanzu dai Iran din bata maida martani ba a kan bukatar ta Amirka da ma hukumar ta AIEA.
Mwallafi: Issoufou Mamane
Edita: Saleh Umar Saleh